Shugaba Mugabe ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da tashar talabijin ta kasar ZBC-TV a daidai lokacin da ake bikin cikarsa shekaru 93 a duniya inda ya ce ba shi da shirin barin mulkin kasar duk kuwa da wadannan shekaru da yake da su.
Rahotanni daga kasar Zimbabwen sun ce a jiya Asabar ne dai aka gudanar da wani gagarumin biki a birnin Bulawayo don taya shugaba Mugaben murnar cika shekaru 93 da haihuwa, bikin da aka ce an kashe kudaden da suka kai kimanin dalar Amurka miliyan guda duk kuwa da matsalolin tattalin arzikin da kasar Zimbabwen take fuskanta.
Cikin 'yan shekarun baya-bayan nan dai shugaba Mugaben wanda yake mulkin kasar Zimbabwen tun daga shekara ta 1980 lokacin da kasar ta sami 'yancin kai, yana ci gaba da fuskantar suka musamman daga 'yan adawan kasar wadanda suke dora alkalin matsalar da kasar take fuskanta a kan shugaba Mugaben.288